Kemi Adetiba | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Kemi Adetiba |
Haihuwa | Lagos,, 8 ga Janairu, 1980 (44 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Yaren Yarbawa |
Harshen uwa | Yarbanci |
Ƴan uwa | |
Mahaifiya | Mayen Adetiba |
Abokiyar zama | Oscar Heman-Ackah (en) |
Karatu | |
Makaranta |
New York Film Academy (en) Jami'ar jahar Lagos Atlantic Hall |
Matakin karatu | Bachelor of Laws (en) |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | music video director (en) , darakta, filmmaker (en) , brand ambassador (en) , mai bada umurni da cinema (en) |
Wurin aiki | Lagos, |
Muhimman ayyuka |
King of Boys The Wedding Party King of Boys: The Return of the King |
Kyaututtuka |
gani
|
Imani | |
Addini | Kiristanci |
IMDb | nm2989430 |
kemiadetiba.com |
Kemi Adetiba Ta kasance yar shirin fim, darekta a telebijin, darektan waka, wanda ayyukan ta ke fitowa a Channel O, MTV Base, Soundcity TV, BET da Netflix.[1][2]
An haife ta a Jihar Lagos ranar 8 Janairun shekarar 1980,[3] Mahaifiyarta itace Mayen Adetiba wacce injinya ce kuma yar'fim. Kemi Adetiba ta fara aikin shirin fim dinta ne tun tana karama inda take gabatar da tallace-tallacen OMO, da bin sawun mahaifin ta, Dele Adetiba.[4]
Kemi ta fara aikin tane a gidan Rhythm 93.7 FM inda take gabatar da shirye-shirye, wanda take gudanar da shirye-shirye kamar su: Soul’d Out da Sunday at the Seaside. Adetiba sannan ta rika yada shirye-shiryen ta a kafafen intanet kamar a Spotify da Soundcloud karkashin sunan 'hule'.
Kemi Adetiba ta fara canja fasalin aiki daga kasancewa mai zance a radiyo zuwa mai gabatar da shirye-shiryen vidiyo a Mnet, wanda ya hada da Studio 53, Temptation Nigeria wanda take gabatarwa tare da Ikponmwosa Osakioduwa. Kemi ta kuma zama mai gabatar da shiri a Soundcity TV da kuma karbar shirin Maltina Dance na tsawon shekaru uku.[5]
Bayan nasarori na tsawon shekaru, Adetiba ta shiga makarantar New York Film Academy dan ta koyi ayyukan da zaisa ta kasance korarriya, ayyukan ta sunsa tazamo shahararriya acikin Afirka da kewayensa. Gajeren shirin Kemi Adetiba film Across a Bloodied Ocean an nuna fim din a 2009 Pan African Film Festival da National Black Arts Festival.[6]
A 8 Satumba 2016, Fim din Kemi Adetiba film na farko da ya shahara "The Wedding Party" (a Nigerian Rom-com film) an nuna fim din amatsayin mabudin taro na Toronto International Film Festival (TIFF), matsayin film din bude City-to-City Spotlight.
A 2017 tana gabatar da shirin "King Women" inda ta tattaunawa da mahaifiyarta Mayen Adetiba. Wasu manyan matan da ta tattaunawa da sun hada da "King Women" included Chigul, Taiwo Ajai-Lycett, TY Bello and Tara Durotoye[7]
Wasu daga cikin Kyautukan data samu sun hada da Best Female Video na wakar "Ekundayo" daga TY Bello a Soundcity TV Music Video Awards, Best Female Video a wakar "Today na Today" na Omawumi a 2010 Nigeria Entertainment Awards. Ayyukan Adetiba na kwananan sun hada da Waje’s "Onye" wanda yayi da Tiwa Savage, Olamide's "Anifowose", "Sitting on the Throne" da kuma Bez's R&B single "Say".
An gabatar da Kemi amatsayin Best Music Video Director of the Year a The Headies 2014.[8] She won the City People Entertainment Award for Best Music Video Director Of The Year (2015)[9] da kuma HNWOTY Award for Woman of the Year a Film da Television (2017)[10]