![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Mutuwa | 27 ga Yuni, 2021 |
Sana'a |
Kenneth Edafe Ogba (1966/1967 – 27 ga watan Yunin 2021) ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisar dokokin jihar Delta mai wakiltar mazaɓar Isoko ta kudu 1 a majalisar dokokin jihar Delta ta 7.
A ranar 9 ga watan Maris ɗin 2019, Kenneth Edafe Ogba, mai wakiltar Peoples Democratic Party ya doke Okiemute Essien na jam'iyyar All Progressives Congress kuma ya lashe kujerar wakiltar mazaɓar Isoko ta kudu 1 a majalisar dokokin jihar Delta. Ya samu ƙuri'u 15,973, yayin da Essien ya samu ƙuri'u 7,323.[1][2][3]
A ranar 10 ga watan Yunin 2019, Ogba ya maye gurbin Orezi Esievo a majalisar dokokin jihar Delta.[4][5]
Ogba daga Oleh, Isoko South, Jihar Delta, Nigeria. Mahaifinsa Lucky Ogba.[6]
Ogba ya mutu a ranar 27 ga watan Yunin 2021 a Oleh, Isoko South, jihar Delta, Najeriya.[7]