![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 14 ga Yuli, 1922 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 4 Disamba 1988 |
Karatu | |
Makaranta |
University of London (en) ![]() |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, Lauya da Marubiyar yara |
Muhimman ayyuka |
Sugar Girl (en) ![]() |
Nathaniel Kolawole Onadipe (Sha hudu 14 ga watan Yulin shekara ta 1922 - hudu 4 ga watan Disambar 1988), wanda aka fi sani da Kola Onadipe, marubucin Najeriya ne wanda aka fi saninsa da littattafan yaransa. [1]
An haifi Kola Onadipe a Ijebu-Ode, Jihar Ogun, a kasar Najeriya . An haife shi a cikin iyalin da suka kasance masu auren mata da yawa kuma shi ne ɗan mahaifiyarsa na biyu. Onadipe ya yi karatun shari'a a Jami'ar London a shekara ta alif dari tara da arba'in da tara 1949 kuma daga baya ya bude kamfanin lauya tare da babban abokinsa Abraham Adesanya . Yana da yara goma sha biyar, yara maza bakwai da 'yan mata takwas, wanda ya sadaukar da rayuwarsa kuma ya tabbatar da cewa sun yi fice wajen samun matsayi na ilimi. Ya mutu yana da shekara sittin da shida a duniya bayan ya kamu da ciwon bugun jini a ranar hudu 4 ga watan Disambar alif dari tara da tamanin da takwas 1988. An binne shi a gidansa na zama a Oyat, Ijebu-Ode, a kasar Najeriya.[2]
Ya kasance Shugaban Kwalejin Olu-Iwa (ɗaya daga cikin manyan makarantun sakandare guda huɗu a Ijebu-Ode a ƙarshen shekarun alif dari tara da arba'in 1940, alif dari tara da hamsin 1950 da farkon shekarun alif dari tara da sittin 1960). Ya kasance mai tsayin daka kuma a horo kuma ya ciyar da makarantar gaba kuma a sawon farko-farko a matakin ilimi da ɗabi'a. Maganarsa mai suna "Ka tafi" wanda ke nufin cewa idan ya kama ka a matsayin mai ba da izini, za a kore ka ba tare da la'akari da ko wane ne iyayinka. Mai makarantar, Cif Timothy Adeola Odutola ya girmama shi sosai.[3]
Yara maza daga ko'ina cikin kasar Najeriya waɗanda aka shigar da su a kwalejin sun zama manyan mutane a ƙarƙashinsa kuma sun tafi manyan cibiyoyin ilmantarwa a gida da wajen kasar don zama manyan shuwagabanni da masu sana'a a rayuwa. Suna da yawa kwarai da gasken da baza a iya ambaton su duka ba.[4]
Ya kasance ya sadaukar lokaci mai yawa a rayuwarsa ga ilimi da rubuta littattafai nayara. Ya rubuta Littattafan yara da yawa wadanda suka hada da: