Kungiyar Kurket ta Saliyo

Kungiyar Kurket ta Saliyo
Bayanai
Iri sports governing body (en) Fassara da cricket federation (en) Fassara
Ƙasa Saliyo

Ƙungiyar Kurket ta Saliyo, Ita ce hukuma mai kula da wasan kurket a kasar Saliyo. Hedkwatar ta a yanzu tana cikin filin wasa na Brookfields National. Ƙungiyar ita ce wakilin Saliyo a Majalisar Cricket ta Duniya[1] kuma memba ce ta kuma ta kasance memba na wannan ƙungiyar tun shekararb2002. Hakanan memba ne na Ƙungiyar Cricket ta Afirka.[2]

Dakarun Royal Artillery na Burtaniya sun gabatar da wasan ga al'ummar kasar a wurare kamar makarantu da sauran cibiyoyi. Makarantar Grammar ta Saliyo da makarantar sakandaren maza ta Methodist su ne makarantu na farko da suka fara wasan motsa jiki a Freetown. Makarantar sakandaren gwamnati ta Bo, wacce aka kafa a shekarar 1906 ta zama makaranta ta farko da ta fara buga ta a larduna. Kasar ta fara buga wasannin kasa da kasa da Gambia a shekarar 1935. Haka kuma an buga gasar kasashen yammacin Afirka tun a shekarun 1930. Daga baya Najeriya da Ghana suma sun shiga cikin kungiyoyin inda suka gyara gasar tsakanin ‘yan mulkin mallaka zuwa gasa hudu na yammacin Afirka da aka fara a shekarar 1967 kuma aka gudanar da su ba bisa ka’ida ba. An maye gurbin gasar da sabon taron taron Arewa maso Yamma NWACC a 2006.[3]

A shekarar 2009 kungiyarsu ta 'yan kasa da shekara 19 ta samu gurbin shiga gasar neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta U-19 ta shekararb2010 a watan Satumba na shekarar 2010 bayan ta kare a matsayi na biyu a gasar cin kofin Afirka na 'yan kasa da shekaru 19 da aka gudanar a kasar Zambia a cikin wannan tsari inda ta doke karin abokan hadin gwiwa a kungiyoyin wasan Cricket na Afirka,[4] duk da haka ba za su iya shiga ba saboda sun kasa isa ƙasar Kanada mai masaukin baki saboda batutuwan visa[5]


  1. "Ireland and Afghanistan ICC newest full members amid wide-ranging governance reform". International Cricket Council. 22 June 2017. Retrieved 1 September 2018.
  2. "Africa Cricket Association".
  3. "Sierra Leone Cricket Association". International Cricket Council. Archived from the original on 2022-10-06. Retrieved 2022-10-06.
  4. "Uganda, Sierra Leone win through". ESPNcricinfo.
  5. "Visa issues end Sierra Leones World Cup dreams".

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]