Leila Zerrougui | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Souk Ahras (en) , 1956 (67/68 shekaru) |
ƙasa | Aljeriya |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya, mai shari'a da Lauya |
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya |
Mamba | United Nations Organization Stabilization Mission in the Democratic Republic of the Congo (en) |
Leila Zerrougui (An haife ta a shekara ta alif 1956), ƙwararriyar yar shari'a ce ta Aljeriya kan haƙƙin ɗan adam da gudanar da shari'a. Ta yi aiki a matsayin wakiliya ta musamman na babban sakataren MDD kuma shugabar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (MONUSCO)[1] tun watan Janairun 2018.
An haife Zerrougui a Souk Ahras. Ta sauke karatu daga L'Ecole Nationale d'administration (Algiers) a shekarar 1980. Tun daga shekarar 1993, ta rike mukamai daban-daban na ilimi a makarantun shari'a a Aljeriya, kuma ta kasance mataimakiyar farfesa a L'Ecole Supérieure de la Magistrature (Algiers). Ta yi rubuce-rubuce da yawa kan yadda ake gudanar da shari'a da hakkin dan Adam.[2]
Ta kasance wakili na musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan yara da rikice-rikice daga watan satumba, shekarar 2012 zuwa watan Mayu, shekarar 2017. A cikin wannan matsayi, ta kasance mai ba da shawara mai zaman kanta don haɓaka wayar da kan jama'a tare da ba da fifiko ga haƙƙin da kare yara maza da mata da rikicin makami ya shafa. .
Ta kasance memba a kungiyar Aiki kan tsare ba bisa ka'ida ba a karkashin Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya daga shekara ta 2001, kuma ta kasance shugabar kungiyar mai ba da rahoto daga shekarar 2003 zuwa watan mayu, shekarar 2008. Kafin wannan, ta dade tana aiki a fannin shari'a na Aljeriya,A shekara ta 2000, an nada ta a Kotun Kolin Aljeriya.
Ta yi aiki a matsayin alkali matashi kuma alkali na farko daga shekarar 1980 zuwa shekarar 1986, sannan ta samu matsayin alkalin kotun daukaka kara daga shekarar 1986 zuwa 1997. Daga shekarar 1998 zuwa 2000, ta kasance mai ba da shawara kan harkokin shari'a ga majalisar ministocin ma'aikatar shari'a, daga shekarar 2000 zuwa 2008 ta samu matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari'a ga majalisar ministocin shugaban Aljeriya. Ta kuma yi aiki a mukamai daban-daban a cikin gwamnatin Aljeriya kuma ta kasance mamba a hukumar da ke kula da harkokin shari'a ta kasar Aljeriya.
Kafin nada ta a matsayin wakiliya ta musamman a shekarar 2012, ta kasance mataimakiyar wakilin babban sakataren MDD kuma mataimakiyar shugabar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (MONUSCO), inda tun a shekarar 2008, ta jagoranci yunkurin tawagar. karfafa bin doka da oda da kare fararen hula. A shekarar 2013 ne Abdallah Wafy ya gaje ta.[3]