Lilian Bach | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Lilian Bola Bach |
Haihuwa | Lagos Island, 1970s (40/50 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, Mai gasan kyau da model (en) |
IMDb | nm1361645 |
Lilian Bola Bach 'yar wasan kwaikwayo ce kuma ƴar Najeriya.[1]
Lilian an haife ta ne a Tsibirin Lagos ga mahaifiya yarbawa kuma mahaifin dan asalin Poland ne. Sakamakon sana’ar mahaifinta, ta zauna a sassa daban-daban na ƙasar a lokacin da take karatunta, ta halarci makarantar yara ta Sojoji, Fatakwal da kuma Makarantar Sakandaren Idi Araba, Legas. Ta yi karatu a takaice a fannin wasan kwaikwayo a Jami'ar Legas Ta rasa mahaifinta yana da shekaru 10.[2][3]
Lilian ta shigo cikin shahara a cikin 1990s a matsayin abin koyi. Ta kuma fafata a gasar Kyawawan Yammata a Nijeriya kuma ta fito a tallan talabijin da yawa, ta zama Fuskar Delta. Ta fara wasan kwaikwayo ne a 1997, inda ta fito a fina -finan Nollywood da yawa na Yarbawa da Ingilishi.