Lucky Aiyedatiwa | |||
---|---|---|---|
24 ga Faburairu, 2021 - 27 Disamba 2023 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ilaje, 12 ga Janairu, 1965 (60 shekaru) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Lucky Orimisan Aiyedatiwa (an haife shi 12 ga Janairu shekarar 1965) ɗan kasuwan Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya yi gwamnan jihar Ondo tun 2023.[1][2] Ya taɓa zama mataimakin gwamnan jihar Ondo daga shekarar shekarar 2021 zuwa 2023 a ƙarƙashin tsohon Gwamna marigayi Rotimi Akeredolu. Tsohon kwamishina ne a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).
A ranar 12 ga Disamba 2023, Aiyedatiwa ya zama muƙaddashin gwamna bayan tafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu yana hutun jinya. Ya taɓa riƙe muƙamin muƙaddashin gwamna daga watan Yuni zuwa Satumba 2023 a lokacin da Akeredolu yake hutun jinya.
An haifi Aiyedatiwa a ranar 12 ga Janairun shekarar 1965, ya fito ne daga Obe-Nla, al’ummar da ke da arziƙin man fetur a ƙaramar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.