Lucy Kibaki | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | mace |
Ƙasar asali | Kenya |
Suna | Lucy |
Shekarun haihuwa | 1940 |
Wurin haihuwa | Central Province (en) |
Lokacin mutuwa | 26 ga Afirilu, 2016 |
Wurin mutuwa | Landan da Cromwell Hospital (en) |
Sanadiyar mutuwa | Sababi na ainihi |
Dalilin mutuwa | Ciwon zuciya |
Mata/miji | Mwai Kibaki (mul) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | First Lady of Kenya (en) da First Lady of Kenya (en) |
Ilimi a | Alliance Girls High School (en) |
Lucy Muthoni Kibaki (ranar 13 ga watan Janairun 1936 - ranar 26 ga watan Afrilun 2016)[1] matar tsohon shugaban Kenya Mwai Kibaki ce kuma ita ce Uwargidan Shugaban Kenya daga shekarar 2002 zuwa 2013.
An haifi Lucy Muthoni a shekara ta 1936. Iyayenta su ne Rev. John Kagai, fasto na Cocin Presbyterian na Gabashin Afirka da Rose Nyachomba, a Mukurwe-ini, gundumar Nyeri, (wanda a da ake kira gundumar Nyeri a Lardin Tsakiya), Kenya.[2] Ta yi karatu a makarantar sakandaren ƴan mata ta Alliance,[3] sannan ta samu horo a matsayin malama, inda ta fara aiki a Kwalejin Malamai ta Kamwenja daga baya kuma a Kwalejin Kambui da ke Kiambu, inda ta kai matsayin shugabar makaranta.[2]
Ta haɗu da Emilio Mwai Kibaki a cikin shekarar 1959. Bayan soyayya ta shekara biyu, sun yi aure a 1961, tare da Lucy ta bar aikin koyarwa a 1963.[2] Sun haifi ƴaƴa huɗu: Judy Wanjiku, Jimmy Kibaki, David Kagai da Tony Githinji. Ta kasance kaka ga Mwai Kibaki jnr Sean Andrew, Rachael Muthoni, da sauransu. Kibaki ya kasance majiɓincin ƙungiyar jagororin mata na Kenya.[4]
Lucy Kibaki ta rasu ne a ranar 26 ga watan Afrilun 2016 a asibitin Bupa Cromwell da ke Landan, bayan gajeriyar jinya a asibitin Nairobi saboda ciwon ƙirji.[2] Ta kasance 80.
An san Lucy don tallafawa marasa galihu da nakasassu.[5] Ta jagoranci ƙungiyar matan shugabannin Afirka 40 da ke yaƙi da cutar HIV/AIDS.[5]