Mahamat Idriss

Mahamat Idriss
Rayuwa
Haihuwa Ndjamena, 17 ga Yuli, 1942
ƙasa Cadi
Faransa
Mutuwa 3 Oktoba 1987
Karatu
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines high jump (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 
Nauyi 75 kg
Tsayi 190 cm

Mahamat Idriss (ne Koundja Ouya, an haifeshi ranar 17 ga watan Yuli, 1942 - ya rasu 3 ga watan Oktoban shekarar 1987) ya kasance ɗan wasan tsalle na ƙasar Chadi.

An haife shi ne a Fort-Lamy, Chadi, French Equatorial Africa.

Sana'a da Nasarori

[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin samun yancin Chadi a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 1960 ya wakilci Faransa, inda ya lashe gasar French National Championship a shekarar 1960 da 1961. [1] Ya kuma zama na goma sha biyu a wasannin Olympics na 1960 yayin da yake wakiltar Faransa. [2]

Ga Chadi ya zama na tara a wasannin Olympic na 1964. A kan Track and Field News cikin jerin zakarun wasannin tsalle da ake fitarwa shekara-shekara sunan Idriss ya fito a matsayin na tara a duniya cikin shekarar 1961, na goma a 1964 har wayau kuma dai na takwas a 1966.

Tsalle mafi tsawo na kansa da ya taɓa yi ya kasance mai tazarar mita 2.17, wanda ya samu damar yi a watan Afrilu 1966 a Fort-Lamy. Wannan har wayau wannan wata gagarumar nasara ce kuma abin tarihi ga Chadi, kodayake ya yi daidai da Paul Ngadjadoum da Mathias Ngadjadoum a shekarun 1993 da 1996 bi da bi.