![]() | |||
---|---|---|---|
2014 - 2016 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jalingo, 10 Nuwamba, 1946 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | mai shari'a |
Mahmud Mohammed, CON, OFR (an haife shi 10 Nuwamba shekara ta alif ɗari tara da arba'in da shida1946A.c). masanin shari'a ne dan Najeriya kuma tsohon Alkalin Alkalan Najeriya.[1][2][3]
An haifi Mai shari'a Mohammed a ranar 10 ga watan Nuwamba 1946.,a Jalingo babban birnin jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya.[4] Ya sami digiri na farko a fannin shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1970, kuma aka kira shi zuwa kungiyar lauyoyin Najeriya, a shekarar da ya kammala makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.[5]
Ya shiga aikin shari’a a lokacin tsohuwar jihar Arewa maso Gabas a matsayin lauya, kuma a shekarar 1991, ya zama babban alkalin alkalan jihar Taraba, a shekarar ne aka tabbatar da nadinsa a matsayin babban alkalin jihar.[6] A 2005, an nada shi mai shari'a a Kotun Koli ta Najeriya.[7] A watan Nuwamba 2014, an nada shi a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya ya gaji Aloma Mariam Mukhtar, mace ta farko a Najeriya.[8] Mai shari'a Mahmud Mohammed shine shugaban majalisar shari'a ta kasa.[4]
|archiveurl=
and |archive-url=
specified (help); More than one of |archivedate=
and |archive-date=
specified (help)
|archiveurl=
and |archive-url=
specified (help); More than one of |archivedate=
and |archive-date=
specified (help)