![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1951 |
Mutuwa | 2021 |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Maishe Maphonya (1951-2021) ɗan Afirka ta Kudu ɗan gwagwarmayar siyasa ne, marubucin wasan kwaikwayo, darekta kuma mawaƙi. An haifi Maponya a Garin Alexandra amma an tilasta masa ƙaura zuwa Diepkloof, Soweto a shekarar 1961.[1]
An haifi Maponya cikin talauci a karkashin mulkin wariyar launin fata a Garin Alexandra, daga baya aka kwashe danginsa da karfi zuwa Diepkloof, Soweto. Ƙaunar karatu da rubuce-rubuce ta taso tun yana ƙarami, wannan ne kuma lokacin da ya zama mai kishin siyasa ya fara rubuta wakoki da shirye-shiryen wasan kwaikwayo waɗanda ke nuna yanayin al'ummar Baƙar fata a Afirka ta Kudu.[2][3]