Makarantar Nahawu CMS da ke Bariga, wani yanki a Legas na jihar Legas, ita ce makarantar sakandare mafi tsufa a Najeriya, wacce Cocin Missionary Society ta kafa a ranar 6, ga Yunin shekarar 1859. Shekaru da dama ita ce babbar tushen limamai da masu gudanar da mulki a Afirka a lokacin mulkin mallaka ta Legas.[1]
James Pinson Labulo Davies ne ya samar da kudaden fara gudanar da makarantar CMS Grammar School, Legas a cikin watan Afrilun shekarar 1859, wanda a watan Afrilun 1859, ya baiwa Babington Macaulay fam 50, (daidai da miliyan ₦1.34 kamar na 2014), don siyan littattafai da kayan aikin makarantar. Tare da tallafin da ya bada, Macaulay ya buɗe Makarantar Grammar CMS a ranar 6, ga Yuni 1859, wanda ya sanya ta zama makarantar sakandare ta farko a Najeriya.[2] A shekarar 1867, Davies ya ba da gudummawar £100 (₦2.68 miliyan kamar na 2014),ga Asusun Gina Makaranta na CMS.[3] Sauran masu ba da gudummawa ga Asusun Gina CMS ba Saros ba ne kamarsu Daniel Conrad Taiwo AKA Taiwo Olowo wanda ya ba da gudummawar £50. Masu ba da gudummawa na Saro Contributors kuma sun haɗa da maza irin su Moses Johnson, IH Willoughby, TF Cole, James George, da Charles Foresythe waɗanda suka ba da gudummawar £40.[4] Makarantar Grammar ta CMS a Freetown, wacce aka kafa a 1848, ta zama abin koyi.
Makarantar ta fara ne da dalibai shida, dukkansu a makarantan kwana a wani karamin ginin bene mai suna 'Cotton House' a unguwar Broad Street. Dalibai da aka fara yayewa sun zamo ma'aikata a makarantan.[1] Manhajar ta ƙunshi Turanci, Logic, Girkanci, Lissafi, Geometry, Geography, Tarihi, Ilimin Bible da Latin.[5] Shugaban makarantar na farko shi ne malami kuma masanin tauhidi Babington Macaulay, wanda ya yi aiki har zuwa mutuwarsa a 1878.[6] Shi ne mahaifin Herbert Macaulay.[7] Lokacin da Birtaniya ta yi mulkin mallaka a Legas a shekara ta 1861, hukumomin mulkin mallaka sun sami mafi yawan ma'aikatansu na gudanarwa na daga mutanen Afirka daga makarantar.[1]
↑ 1.01.11.2"School History". Old Grammarians Society. Archived from the original on 19 September 2008. Retrieved 21 May 2011.
↑Elebute, Adeyemo. The Life of James Pinson Labulo Davies: A Colossus of Victorian Lagos. Kachifo Limited/Prestige. p. 190. ISBN9789785205763.
↑Herskovits Kopytoff, Jean. A preface to modern Nigeria: the "Sierra Leonians" in Yoruba, 1830–1890. University of Wisconsin Press, 1965. p. 244.
↑Herskovits Kopytoff, Jean. A preface to modern Nigeria: the "Sierra Leonians" in Yoruba, 1830–1890. University of Wisconsin Press, 1965. p. 365 note 87.
↑Ambassador Dapo Fafowora (4 June 2009). "150 years of the CMS Grammar School, Lagos". The Nation (Nigeria). Archived from the original on 3 October 2009. Retrieved 21 May 2011.
↑"Macaulay, Thomas Babington 1826 to 1878 Anglican Nigeria". Dictionary of African Christian Biography. Archived from the original on 19 August 2014. Retrieved 23 January 2015.
↑"Brief History of CMS Grammar School". CMS Grammar School. Retrieved 21 May2011.