![]() | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | 1980 (44/45 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Botswana | ||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Harshen Tswana | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | gwagwarmaya da Mai kare ƴancin ɗan'adam | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Kyaututtuka |
gani
| ||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||
Addini | Kirista |
Malebogo Molefhe (an haife a shekara ta c. 1980) 'yar wasan ƙwallon kwando ce na Motswana wanda ta zama mai fafutukar yaƙi da cin zarafin jinsi bayan an harbe ta sau takwas. A shekarar 2017, ta sami lambar yabo ta Mata masu ƙarfin gwiwa.
An haifi Molefhe a shekara ta 1980. An zaɓe ta ne domin ta wakilci ƙasarta a wasan ƙwallon kwando, inda take buga wasanni da ƙwarewa tun tana shekara 18. Tana zaune a Manyana.
Malebogo ta girma a kasar Botswana dake kudancin Afirka kuma tana zaune a kudancin Gaborone. Tsohon saurayinta ya kai mata hari a shekara ta 2009, lokacin tana da shekaru 29. [1] A harin, saurayinta ya harbe ta har sau takwas. Maharin, wanda aka bayyana a matsayin "deranged", sannan ya harbe kansa har lahira.[2] Malebogo ta tsira kuma ta murmure daga harin, amma yanzu tana amfani da keken guragu [3] saboda rauni a kashin baya. [4]
Malebogo ta zama mai ba da shawara ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jinsi (GBV) da cin zarafin gida a gidan rediyon Botswana. Ta shirya tarurrukan karawa juna sani tare da samar da horo tare da kungiyoyin jiha da masu zaman kansu a Botswana. Ta fahimci cewa akwai al'amuran al'adu da suka kasa hana GBV kuma ta ba da gudummawa don wayar da kan jama'a game da bukatar canji.
Malebogo ta koyar da yara mata game da girman kai don ba su damar yin tsayayya da zaluncin jinsi da sauran nau'ikan cin zarafin gida. Ita da Ma'aikatar Ilimi ta Botswana sun ƙirƙiri wani shiri don yara don taimakawa koyo game da GBV a cikin gida. Malebogo kuma tana ƙarfafa para wasanni da wasanni ga mata gabaɗaya.
A ranar 29 ga watan Maris 2017 ita da wasu mata 12 na wasu ƙasashe sun sami karbuwa daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka kuma an ba ta lambar yabo ta Mata masu ƙarfin gwiwa a Washington, DC[5] Ita ce macen Botswana ta farko da ta sami irin wannan lambar yabo.[6] Kamar yadda asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar, fiye da kashi biyu bisa uku na matan Botswana sun fuskanci wani nau'i na cin zarafin mata a rayuwarsu.[7]