Manandafy Rakotonirina | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Fandriana (en) , 30 Oktoba 1938 (86 shekaru) | ||
ƙasa | Madagaskar | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Malagasy Revolutionary Party (en) |
Manandafy Rakotonirins (30 Oktoba 1938 - 15 Maris 2019[1][2]) ɗan siyasan Malagasy ne. Ya kasance babban jigo a siyasance a Madagascar tun a shekarun 1970, kuma a watan Afrilun 2009 hambararren shugaban kasar Marc Ravalomanana ya nada shi a matsayin firaminista.
An haife shi a Fandriana, Amoron'i Mania, ya sami karatun firamare da sakandare a Ambositra da Antsirabe kuma ya halarci Jami’ar Antananarivo. Daga nan ya zama mataimaki a Ecole Nationale Supérieure d'Agronomie kuma Farfesa a fannin zamantakewa. A matsayinsa na tabbataccen ɗan gurguzu, ya shiga jam'iyyar Madagasikara Otronin'ny Malagasy party, [3][4] a cikinta ya yi kira da a shigar da proletariat Antananarivo.[5]