Maraq | |
---|---|
miya | |
Tarihi | |
Asali | Somaliya |
Maraq (Larabci : مرق) abinci ne na Yaman. Ya samo asali ne daga Yemen. Hakanan ana samun wannan abincin a Somaliya, Oman da Indonesia. [1]
Kalmar kanta tana nufin " broth " a cikin harshen Larabci.
Yadda ake dafa maraq yawanci ana farawa ne da tafasa nama tare da kayan yaji da albasa. Bayan naman ya yi laushi kuma ya dahu, sai a kai shi kan gadon shinkafa. Za a yi amfani da broth maraq da aka samu a cikin kwano a gefe. Hakanan ana yawan matse lemun tsami a cikin maraq yayin da yayi sanyi don ƙarin ɗanɗano. Ana kuma iya samun Maraq a cikin Somaliya, Habasha, Oman, Yemen da sauran ƙasashen Larabawa a yankin Tekun Fasha. Hakanan ana iya samunsa a Indonesia. [2] [3]