Margaret Sekaggya | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kampala, 23 Oktoba 1949 (75 shekaru) |
ƙasa | Uganda |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Makerere Jami'ar Zambia |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Margaret Sekaggya lauya ce 'yar ƙasar Uganda kuma mai fafutukar kare hakkin bil'adama. Daga shekarun 2008 zuwa 2014, Sekaggya ita ce wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan masu kare hakkin ɗan Adam.[1][2]
An haifi Sekaggya a Kampala a ranar 23 ga watan Oktoba 1949. A shekara ta 1970, ta fara karatu a Jami'ar Makerere tana neman digiri na farko a fannin shari'a. A shekara ta 1990, ta sami digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Zambia. Ta yi aiki tare da gwamnatocin Uganda, Zambia, da Majalisar Ɗinkin Duniya. Daga shekarun 1996 zuwa 2009, ta kasance shugabar hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Uganda.[3][4] A cikin shekara ta 1995, an naɗa ta alkaliya a Babban Kotun Uganda. A wannan lokacin, an zaɓe ta ne domin ta kula da hukumar zaɓen ƙasar Uganda.[5][6] Ta kuma shiga cikin fitar da kundin tsarin mulkin Uganda na 4 a shekarar 1995. A cikin shekarun 80s, ta kasance mai tushe a Cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya a Namibiya, tana shirya cibiyoyin Namibiya don samun 'yancin kai. Daga shekarun 1978 zuwa 1982, ta kasance alkaliya mai tushe a Lusaka. [7] [8] Daga shekarun 2008 zuwa 2014, Sekaggya ita ce wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya nlta musamman kan masu kare hakkin ɗan Adam. [9]