Martha Ankomah | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Accra, 10 Oktoba 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta | Labone Senior High School (en) |
Harsuna |
Turanci Twi (en) |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Muhimman ayyuka |
Heart of Men (fim) Somewhere in Africa |
Kyaututtuka | |
Ayyanawa daga | |
IMDb | nm4718345 |
Martha Ankomah(an haife ta a ranar 10 ga watan oktoba shekarar 1985) ta kasance yar'Ghana, yar'fim da gudanar da kasuwanci. [1][2]
Ankomah an haife ta ne a Accra, Ghana, amatsayin na fari gurin mahaifiyarta, Ankomah tana tuna irin wahalhalun da tasha yayin girmar ta.[3] Ita tsohuwar daliba ce ta Adabraka Presbyterian Junior High School, Labone Senior High School da Jami'ar Kwaleji na Jayee.[4]
Ta fadi cewa ta fara aikin fim ne a 1994. Bayan ta yi fina-finai da dama, da fitowa a television serials, ta shiga Next Movie Star, a nan ne Aka sa tazama a 2007 edition na reality show. Ankomah ta bayyana a yayin hira da tayi da Hitz FM a shekarar 2016 zata rika fitowa ne kawai a shirye-shiryen da suka face da dabi'u nagari.[4] In September 2018, cewa zata iya fitowa a kowane mataki, idan har matakin zai tura sako mai kyau zuwa ga masu kallo.[5] [6][7]
A 2014, Ankomah ta sanya hannu yarjejeniyar kasuwanci da Vitamilk Viora.[9] Dusk Capital Limited, dake Ghanaian Investment Bank a 2017 Ankomah ta bayyana cewa ta zama jakadiyar kamfanin.[10] Ta kuma yi aiki da kamfanin Globacom tun daga 2018 amatsayin jakadiyar tallace-tallace.[11] A 2018, Ankomah ta zama jakadiyar tallace-tallace na Ghana Textiles Printers' (GTP) a sabon atamfar 'Adepa Dumas'.[12][13]
A watan Yulin 2013, Ankomah ta bude shago kwalliyar ta mai suna 'Martha's Place' a Accra. Inda take kula da mata da maza.[14]
Gidauniyar Martha Ankomah ta kafa ta ne a 2016, a Ackrobon dake a Awutu Senya District.[15]
Gidauniyar na aiki Dan magance Autism tare da jakadu da zasu wayar da Kai akan autism da tallafawa da taimakon yara[16]
|website=
(help)