![]() | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Gabon, 1 Satumba 1996 (28 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya |
Medwin Biteghe (an haife shi a ranar 1 ga watan Satumban shekarar 1996) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Gabon wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Al-Sahel ta Saudi Arabiya. [1] [2]
Biteghe ya buga wasa a Cercle Mbéri Sportif a gasar Gabon Championnat National D1 na shekarar 2015.[3] Ya jagoranci kulob din zuwa wasan kusa da na karshe na shekarar 2016 Coupe du Gabon Interclubs.[4] A ranar 29 ga watan Yuni 2022, Biteghe ya koma kulob din Al-Sahel na Saudiyya. [5]
Biteghe ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Gabon kwallo a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2017 da Mali a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018 da suka tashi 0-0 a gida a Stade de Franceville.[6]