Milena Balsamo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bologna (en) , 26 ga Janairu, 1961 (63 shekaru) |
ƙasa | Italiya |
Karatu | |
Harsuna | Italiyanci |
Sana'a | |
Sana'a | Paralympic athlete (en) |
Kyaututtuka |
Milena Balsamo (an haife ta 26 Janairu, 1961 Bologna). ita 'yar wasan Paralympic ce ta Italiya.
Ta yi gasa a keken guragu a matsayin mai tsere a rukuni na 4, kuma ta halarci wasannin nakasassu na1984, na Stoke Mandeville, da na nakasassu na bazara na 1988, a Seoul, inda ta lashe lambobin yabo guda biyar, gami da hudu a cikin relay.[1]
A cikin 2015, an ba ta lambar yabo ta Collare ,d'oro saboda cancantar wasanni daga kwamitin Olympics na Italiya.[2]
An haife ta a Bologna. An horar da ta a cikin San Michele Society.
Ta ci lambar tagulla a wasannin nakasassu na bazara na 1984, a cikin mita 4x400,[3] da lambar azurfa a mita 100.[4] Ta lashe lambar zinare a wasannin nakasassu na lokacin rani na 1988 a cikin mita 4x100,[5] da lambar tagulla a mita 4x200,[6] da mita 4x400.[7]
A shekarar 1992, ta bar gasar kasa da kasa.