Mohamed Abou Gabal | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Asyut (en) , 29 ga Janairu, 1989 (35 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Misra | ||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Larabci Egyptian Arabic (en) | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai tsaran raga | ||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.96 m | ||||||||||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||||||||||
Addini | Musulunci |
Mohamed Qotb Abou Gabal Ali (Larabci: محمد قطب أبو جبل علي; an haife shi 29 ga Janairun shekarar 1989), wanda kuma aka fi sani da Gabaski, kwararren dan wasan kwallon kafa ne na kasar Masar wato Egypt wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a kulob din Zamalek na Premier na Masar da kuma tawagar kasar Masar.[1]
Gabaski ya kasance cikin tawagar Masar don gasar Afcon 2021 (wanda aka gudanar a 2022). An kawo shi ne a matsayin wanda zai maye gurbinsa a karawar da Masar ta yi da Ivory Coast a zagaye na 16. Ya ceci bugun daga kai sai mai tsaron gida Eric Bailly, inda ya taimakawa Masar ta ci gaba. A wasan daf da na kusa da na karshe Gabaski ya fara wasan amma an sauya shi a cikin karin lokaci saboda raunin da ya samu a tsoka, duk da cewa kungiyarsa ta yi nasara a wasan. A wasan dab da na kusa da na karshe ya ceci bugun fanareti biyu daga Kamaru sannan ya taimakawa Masar ta kai wasan karshe.
Bugu da kari, ya kuma ture fenaritin mane a wasan karshe na AFCON.[2]
ENPPI
Zamalek