Mohammed Shaaba Lafia

Mohammed Shaaba Lafia
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 -
District: Kwara North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2011 -
District: Kwara North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2011 -
District: Kwara North
gwamnan jihar Kwara

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Alwali Kazir - Mustapha Ismail
District: Kwara North
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta University of Wisconsin–Madison (en) Fassara
Jami'ar Ibadan
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

An zaɓi Sha’aba Lafiagi a matsayin gwamnan jihar Kwara a watan Janairu a shekara ta 1992 a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), kuma gwamnatin Janar Sani Abacha ta tsige shi daga mukaminsa a watan Nuwamba a shekara ta 1993.[1]

A matsayinsa na gwamna ya ƙaddamar da gina sabbin hedikwata na kamfanin buga takardu da buga littatafai a jihar Kwara, amma ba a bude su ba sai a shekara ta 2002, kuma a shekarar 2010 aka shirya rugujesu.[2]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance Mai bada tsaro ga Olusola Saraki, shugaban sanatocin lokacin Nigerian Second Republic, wanda ya taimake shi yazamo zaɓaɓɓen gwamna a watan Disambar a shekara ta 1991. Ya taba zama memban kwamitin ƙidaya na ƙasa (CNC) tare da to Olusola Saraki daga baya ya bar saraki inda ya bayyana yana goyon bayan Mohammed Lawal don zama gwamnan jahar Kwara a shekara ta 1999.[3] Duk da haka, Yana da karfi a siyasar jihar Kwara.[4]

Lafiagi ya zama mamba a kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP.[5] A cikin watan Fabrairun shekaar 2009, an naɗa shi shugaban Majalisar Cigaban Ciwon sukari ta ƙasa, mai fafutuka.[6] Ya jagoranci kwamitin tsare-tsare na taron ƙasa na musamman na jam’iyyar PDP na ranar 20 ga watan Afrilu, shekara ta 2009, inda ya ba da shawarar a kashe Naira miliyan 400. Idan aka yi la’akari da yanayin tattalin arziki, Shugaba Umaru ‘Yar’aduwa ya rage kasafin zuwa Naira miliyan 100.[7]

A watan Afrilun shejara ta 2011, an zabe shi Sanata mai wakiltar Kwara ta Arewa Sanata