Mohammed Tasiu Ibrahim | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1 Oktoba 1961 (63 shekaru) |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Tsaron Nijeriya |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Digiri | Janar |
Mohammed Tasiu Ibrahim (an haife shi ranar 1 ga Oktoban shekarar 1961). Manjo Janar ne na sojan Najeriya mai ritaya wanda ya yi aiki a matsayin Kwamanda na 27 a Kwalejin Tsaro ta Najeriya. An naɗa shi Kwamanda a watan Yulin shekarar 2015 ta hannun babban hafsan sojin ƙasa, Maj-Gen Tukur Yusuf Buratai[1] wanda ya gaji Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris.[2]
An haifi shi ranar 1 ga watan Oktoban 1961, a Gumel, Jihar Jigawa.[3] Ya halarci makarantar firamare ta Gumel Gabas a garin Gumel sannan ya kammala firamare a Tudun-jukun Primary School Zaria 1974. Ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Giwa, Zaria daga 1974 zuwa 1979 inda ya samu takardar shedar Sakandare ta Yammacin Afrika (WAEC).
Bayan ya yi aiki na shekara guda (tsakanin 1979 zuwa 1980) da First Bank of Nigeria da ke Kano ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a matsayin memba na kwas na 29 na yau da kullun (ciki har da sauran hafsoshi irin su Tukur Yusuf Buratai ) daga Janairu 1981 zuwa Disamban shekarar 1983., lokacin da ya karɓi kwamandan aikin sojan Nijeriya a matsayin Laftanar na biyu.[3]
Janar Ibrahim ya taɓa riƙe muƙamin Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya na Sashen Tattalin Arziƙi na Ƙasa kafin a naɗa shi Kwamandan NDA.[1] Ya yi ritaya daga aikin sojan Najeriya a watan Oktobar 2017.[4]