Muhammad Ali Mirza | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jhelum (en) , 4 Oktoba 1977 (47 shekaru) |
ƙasa | Pakistan |
Sana'a | |
Sana'a | mechanical engineering (en) da mechanical engineer (en) |
Imani | |
Addini | Musulunci |
ahlesunnatpak.com |
Muhammad Ali Mirza an haife shi a ranar 4 ga watan Oktoba shekara ta 1977), wanda aka fi sani da Injiniya Ali Mirza, ko kuma ta hanyar sunansa na farko kamar EMAM, Malamin addinin Musulunci ne a kasar Pakistan kuma YouTuber . [1][2] Injiniya ne ta hanyar sana'a, a san shi da laccocinsa kan batutuwan addini, wanda ya jawo hankalin rikice-rikice da yawa, gami da yunkurin saɓo a shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023.[3]
An haifi Muhammad Ali Mirza a ranar 4 ga watan Oktoba shekara ta 1977 a Jhelum, Punjab . Mahaifinsa, Mirza Arshad Mahmud, an ruwaito cewa yana aiki a Bankin Allied. Ali Mirza ya sami karatunsa a matsayin injiniya daga Jami'ar Injiniya da Fasaha, Taxila . Ya yi aiki a matsayin injiniyan Gwamnatin Punjab a kan ma'auni na albashi na 19 amma daga baya ya bar aikin da sashen ya nemi ya bari saboda ya zama mutum na jama'a.[4][5][6]