Muhammad Sanneh | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Serekunda (en) , 19 ga Faburairu, 2000 (24 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Gambiya | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 180 cm |
Muhammed Sanneh (an haife shi a ranar 19 ga watan Fabrairu a shekara ta 2000) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Baník Ostrava.
A ranar 2 ga watan Fabrairu a shekara ta 2019, Sanneh ya bar ƙasarsa ta Gambia kuma ya sanya hannu kan kwangilar ƙwararru tare da Paide. [1] A cikin watan Disamba a shekara ta 2020, an sanya shi cikin ƙungiyar Meistriliga na kakar saboda rawar da ya taka a kakar shekarar 2020.[2] Ya shiga tawagar Czech Baník Ostrava a cikin watan Janairu a shekara ta 2021. [3] Ya fara wasansa na farko na ƙwararru tare da Baník Ostrava a wasan 1 – 1 Czech First League da Bohemians 1905 a ranar 16 ga watan Afrilu a shekara ta 2021. [4] Baník Ostrava ya kunna batun siyan sa akan lamunin nasa, don ci gaba da kasancewa tare da kulob din bayan kakar 2020 zuwa 2021 a ranar 17 ga watan Afrilu a shekara ta 2021.[5]
A cikin watan Janairu a shekara ta 2021, Sanneh ya sanya hannu kan lamunin rabin kakar tare da kulob ɗin Pohronie.[6]
A watan Yuni a shekara ta 2020, Sanneh ya sami kiransa na farko ga babban tawagar ƙasar Gambia.Ya buga wasa a Gambia a wasan sada zumunta da suka doke Togo da ci 1-0 a ranar 8 ga watan Yuni a shekara ta 2021.[7]
Kanin Sanneh Bubacarr shima kwararren dan wasan kwallon kafa ne. [8]