Musa Mohammad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bagan Datuk (en) , 29 Nuwamba, 1943 |
ƙasa | Maleziya |
Mutuwa | Petaling Jaya (en) , 8 ga Yuni, 2024 |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | United Malays National Organisation (en) |
Tan Sri Dato 'Seri (Dr.) Musa bin Mohamad [1] ( Jawi : موسى بن محمد) ya kasance ɗaya daga cikin membobin Majalisar Koli ta UMNO a tsakanin 2000 da 2003. Ya kuma kasance tsohon Ministan Ilimi kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kwalejin, Universiti Sains Malaysia .
Ya sami Digiri na farko a kan ilimin hada magunguna (wato pharmacy) a Jami’ar Singapore [2] a 1962 da kuma Master of Science Degree a Pharmaceutical Technology daga Jami’ar London a shekarar 1972.
Musa Mohammad ya kware a fannin koyarwa da gudanarwa na tsawon shekaalru 20 a Universiti Sains Malaysia. Har wayau ya rike matsain Dean na Pharmacy na Universiti Sains Malaysia (USM) daga shekarar 1975 to 1979. Ya kuma riqe matsayin Deputy Vice Chancellor (Academic) kafin a bashi Vice Chancellor from 1982 to 1998.
Firayim Ministan Malaysia, Tun Dr. Mahathir Mohamad ne ya nada shi matsayin Sanata a shekarar 1999. Sannan, an nada shi matsayin Ministan Ilimi daga 1999 zuwa 2003. Tun Abdullah Ahmad Badawi ya tsawaita mukaminsa na minista har zuwa 2004.
Bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati, an nada shi a matsayin Shugaban wasu kamfanoni kamar Polyglass, Universiti Telekom Sdn Bhd (shi ma darekta). Ya kuma kasance Shugaban Kamfanin Mai Zaman Kansu & na Shugabancin Pelikan International Corporation Berhad daga 2005 zuwa 2012.
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jami'ar (KUSTEM), Jami'ar Malaysia Sabah (UMS), Kwalejin Kwalejin Injiniya ta Arewacin Malaysia (KUKUM) ta ba shi digirin girmamawa na 7 a fannin kimiyya; a cikin ilimin fasaha ta Jami'ar Multimedia (MMU); a cikin falsafar ta Kwalejin Jami'ar Tun Hussein Onn (KUITTHO); da ilimi ta Jami'ar UCSI. Tan Sri Musa shi ma ya kasance ɗan’uwan ƙungiyar likitancin Malaysia ne da Kwalejin Kimiyya. [3]