Myriam Léonie Mani (an haife ta a ranar 21, ga watan Mayu 1977) 'yar wasan Kamaru ce wacce ta kware a tseren mita 100 da 200. [1]
Mani ta wakilci Kamaru a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2008 da ta fafata a gudun mita 100. A zafafan wasanninta na farko ta zo na uku bayan Torri Edwards da Jeanette Kwakye a dakika 11.64 domin tsallakewa zuwa zagaye na biyu. A can ta ƙasa tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshe saboda lokacinta na 11.65 shine karo na shida na zafi, wanda ya haifar da kawar da ita. [1]