Nair Almeida | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Lobito, 23 ga Janairu, 1984 (40 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Angola | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | handball player (en) | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||
Tsayi | 181 cm |
Nair Filipe Pires de Almeida (an haife ta a ranar 23, ga watan Janairu shekara ta 1984 a Lobito, lardin Benguela ), 'yar wasan ƙwallon hannu ce ta kasar Angola mai ritaya. Almeida ta fara aikinta a wata karamar kungiyar kwallon hannu mai suna Escola de Andebol da Restinga, do Lobito (EARL). [1] Ta yi takara a gasar Olympics ta bazara a shekarar 2004 a Athens da kuma gasar cin kofin duniya ta shekarar 2005.[2] A gasar cin kofin duniya ta 2007 Angola ta zama ta 7, yayin da Almeida ta zura kwallaye 57 kuma ita ce ta shida a jerin ‘yan wasan da suka fi zura kwallaye. Ta taka leda a kasar Angola a gasar Olympics ta bazara a shekarar 2008 da aka yi a birnin Beijing da kuma gasar lokacin rani ta shekarar 2012 da aka yi a birnin London. [1]