![]() | ||||
---|---|---|---|---|
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Yobe | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 980 km² |
Nangere ƙaramar hukuma ce dake a jihar yobe. Arewacin Najeriya. Hedkwatarta dake a garin Sabon Gari Nangere (ko Sabon Garin) a kan hanyar zuwa Gashu'a daga fotiskum a11°51′50″N 11°04′11″E / 11.86389°N 11.06972°E.
Karamar hukumar Nangere tana da girman kilomita murabba'i dari tara da tamanin 980 kuma tana da matsakaicin yanayi na zafi/sanyi na 34 °C. Karamar hukumar ta nada manyan yanayi guda biyu da suka hada da rani da damina yayin da aka kiyasta yawan ruwan sama a yankin ya kai milimita dari tokas da shasa'in (890) na ruwan sama a shekara.[1]
Garin na da jimillar yawan jama'a 87,823 a Kidayar shekara ta 2006.
Nangare na da lambar akwatin gidan waya na yankin ita ce shida uku daya (631).[2]
Sauran garuruwa da kauyukan da suka hada da karamar hukumar Nangere sun hada da Dawasa, Tagamasa, Sabon Gari Nangere, Tikau, da Dorowa.
Yawancin mazauna Nangere suna gudanar da ayyukan noma. Ana noman amfanin gona iri-iri a karamar hukumar yayin da ake kiwon dabbobi da sayar da su a yankin. Har ila yau ciniki ya bunkasa a karamar hukumar Nangere
inda yankin ke da kasuwanni da dama inda ake saye da sayar da kayayyaki iri-iri. Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da jama'ar karamar hukumar Nangere ke gudanarwa sun hada da farauta, sana'ar fata da sana'o'in hannu da sauran su.