National Patriotic Front of Liberia | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | jam'iyyar siyasa |
Ƙasa | Laberiya |
National Patriotic Front of Laberiya (NPFL) kungiya ce ta 'yan tawayen Laberiya wacce ta fara kuma ta shiga yakin basasa na farko na Laberiya daga 24 Disamba shekara ta 1989 zuwa 2 ga Agusta shekara ta 1997. NPFL ta samu daga tashin hankali na kabilanci da tashin hankali na jama'a saboda gwamnatin Laberiya wanda aka siffanta ta da kama-karya, cin hanci da rashawa, da nuna son kai ga kabilar Krahns. NPFL ta mamaye Laberiya ta kan iyakar Ivory Coast da gundumar Nimba a Laberiya karkashin jagorancin Charles Taylor, [1] tsohon dan siyasar Laberiya kuma jagoran 'yan daba wanda ya yi aiki a matsayin shugaba na 22 na Laberiya daga 2 Agusta shekara ta 1997 har zuwa murabus dinsa a kan 11 Agusta shekarar 2003.
NPLF ita ce ke da alhakin ɗimbin laifuffukan yaƙi da laifuffukan cin zarafin ɗan adam, waɗanda suka haɗa da kisan jama'a, fyade, bautar jima'i, shigar da yara aikin soja, azabtarwa, da kisan gillar siyasa. Take haƙƙin ɗan adam sama da 60,000 da NPFL ta yi an rubuta shi bisa hukuma ta Liberian Truth and Reconciliation Commission[2][3]
Charles Taylor ne ya jagoranci bangaren soji na NPFL, wanda ya umurci NPFL da ta dauki makamai don yakar gwamnatin Samuel Doe a ranar 24 ga Disamba shekara ta 1989. Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta kasance shugabar Laberiya ta 24 daga 16 ga Janairu shekara ta 2006 zuwa 22 ga Janairu shekara ta 2018, itace ce Kodinetan kasa da kasa na NPFL kuma ta taimaka wajen tara kudi ga kungiyar 'yan tawaye. Daga baya Sirleaf ta yi watsi da Taylor kuma ta ci gaba don samun lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel saboda goyon bayan gwagwarmaya ta zaman lfy don kare lafiyar mata don shiga aikin samar da zaman lafiya.[4] Tom Woewiyu ya yi aiki a matsayin ministan tsaro kuma mai magana da yawun kungiyar ta NPLF kuma ya yi aiki don tabbatar da manufa da tsare-tsaren kungiyar 'yan tawayen ga manyan jami'an kasashen waje.[5] Martina Johnson ta kasance ɗaya daga cikin kwamandojin layin gaba na NPFL kuma an zarge ta da hannu kai tsaye wajen lalata da kashe mutane a ƙarshen shekarar 1992 yayin wani harin NPFL da aka fi sani da Operation Octopus.[6][7]