Nelly Karim ƴar mahaifiyar Rasha ce ta Soviet daga Leningrad kuma mahaifinta ɗan Masar ne daga Zagazig. Ta faɗa a wata hira da 'yar jarida Nishan cewa kyawunta, ba daga asalin Rasha ba, kuma tana kama da mahaifinta. Tana da ɗan'uwa ɗaya wanda ya girme ta, sunansa Ashraf ne wanda likita ne kuma ya yi ƙaura zuwa Amurka. Ta zauna tare da iyalinta a Rasha har zuwa shekara 16 amma ta yi hutun makaranta tare da iyakarta a Alexandria, Misira.
Nelly Karim ta gabatar da fin din Kurkukun mata (Turanci: Women's prison), inda wannan fin ya kasance mafi samun karbuwa a gurin 'yan kallo. Kasancewar ta sananniyar Tauraruwar fina-finai.[6]