Nikoletta Samonas | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Accra, 5 Satumba 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta |
Holy Child High School, Ghana (en) Kwame Nkrumah University of Science and Technology |
Matakin karatu | Bachelor of Arts (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da model (en) |
Muhimman ayyuka |
Desperate Measures (en) Q56315930 Love and Bullets (en) Potato Potahto V Republic The Will (en) My First Wife (en) Things We Do for Love (en) Ladies and Gentlemen (en) Pretty Queen (en) |
IMDb | nm4382673 |
Nikoletta Samonas (an haife ta biyar 5 ga watan Satumba shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985) yar wasan kwaikwayo ce ƴar Ghana kuma ƴar wasan kwaikwayo ce mai zaman kanta. An san ta da Nikki Samonas a masana'antar nishaɗi kuma ta yi rawar gani a cikin fina-finai da yawa.[1] Ita tsohuwar daliba ce a makarantar Holy Child High School da kuma Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.[2]
Samonas ta yi karatun ta na asali a DEKS (Discipline, Excellence, Kindness, Service) International School a Tema kuma ta ci gaba da zuwa Holy Child High School don babbar makarantarta inda ta karanta fasahar gani.[2]
Daga nan ta ci gaba da karatunta na sakandare a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah sannan ta kammala karatun digiri na farko a fannin fasahar sadarwa.[2]
Ta yi aiki a gidajen shirye-shiryen TV daban-daban kamar CharterHouse wanda ta dauki nauyin Rythmz, Farm House Production wanda ta dauki nauyin shirin African Movie Review Show kuma ta dauki nauyin Breakfast Live, shirin talabijin na safe a TV Africa.[3][4]
Nikki Samonas ita ce jakadan UNHCR na farko na Ghana tare da Kwame Annom. Ta kuma yi rawar gani a matsayin Babban Mai Tasiri a cikin kamfen na LuQuLuQu na UNHCR.[5]
An karrama ta ne daga 3G Awards 2019 a New York saboda gudunmawar da ta bayar ga masana'antar fina-finai da nishaɗi ta Ghana.[10]