Nok wani kauye ne dake Jaba, karamar hukumar Jaba a Jihar Kadunan Nijeriya. Samun surar halittu da akayi da yambu a garin yasa aka rika amfani da suna garin yazama nan ne al'adun Nok take, wadanda surorin su sune aka rika yin su a Nijeriya tun a shekarar 1500 BC zuwa 500 AD.[1][2] An gano wadannan sarrafofin hannun ne a shekarar 1943 lokacin gudanar da aikin hako ma'adinai.[3] Mai aikin Bernard Fagg ya binciki garin da kuma taimakawan yangarin ne yasa aka hako Karin surarin da da dama.[4] kayayyakin kona karafa na kira suma ansame su a lokacin.[1] lokutan da aka fara binciken garin tun kafin a fara aikin Kira ansamu konannun katakai a tsakiyar garin Nok, a shekarar 1951,ance katakan zasu kai tun shekara ta 3660 BC, amma ana ganin akwai matsalar ta yadda aka tabbatar da hakan.[5]
-
Gunkin Nok
-
Gunkin Nok a Kudancin Kaduna
-
Fuskan Gunkin Nok
-
Gunkin a gidan tarihi
-
Iyakan da Nok take da yawan Jama'a
-
Tsohuwar garin Nok a Kaduna