Omar Assar | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Desouk (en) , 22 ga Yuli, 1991 (33 shekaru) |
ƙasa | Misra |
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) |
Karatu | |
Harsuna |
Larabci Egyptian Arabic (en) |
Sana'a | |
Sana'a | table tennis player (en) |
Mahalarcin
| |
Tsayi | 196 cm |
Omar Assar An haife shi a ranar 22 ga watan Yuli 1991 a Desouk ɗan wasan table tennis ne na ƙasar Masar.[1] Ya lashe azurfa guda da zinare a wasan kungiya a gasar Larabawa ta shekarar 2011 a Doha. Ya kuma taka leda a gasar Olympics ta bazara na shekarun 2012 da 2016 a cikin gasar maza kadai, amma an ya sha kashi a zagaye na biyu a lokuta na biyu. [2] [3]
A gasar wasanni na duniya wato Olympics ta lokacin rani ta 2012 Assar ya fafata a gasar ta maza, inda ya sha kashi a zagaye na biyu a hannun Panagiotis Gionis, da gasar maza, inda Masar ta sha kashi a zagayen farko da Austria.
A Gasar Olympics ta lokacin bazara ta shekarar 2016 Assar ya fafata a cikin gasar men's singles kawai. Ya sake yin rashin nasara a zagaye na biyu, a wannan karon da kyar ya sha kashi a hannun Lei Kou ta Ukraine da ci 3-4.
Gasar Cin Kofin Duniya ta ITTF 2017
Men's singles
Assar ya fafata ne a gasar cin kofin table tennis ta duniya a shekarar 2017, mai lamba 50, inda ya fafata da dan wasan Italiya Marco Rech a zagayen farko, wanda ya doke shi a wasan kusa dana karshe (4-3), bayan da ya yi rashin nasara a wasanni 3 na farko. A zagaye na biyu, dan wasan Hong Kong ya doke shi, kuma mai lamba 7 Wong Chun Ting (2-4).
Men's doubles
Assar ya hada kai tare da dan wasan Masar Mohamed El-Beiali don wasan biyu, inda ba a saka su ba kuma sun fuskanci lamba 5 dan Brazil Hugo Calderano da Gustavo Tsuboi, sun sha kashi da (2-4).
"Mixed doubles"
Assar ya haɗu tare da 'yar wasan Masar Dina Meshref don wasan mixed doubles, wanda aka tsara a matsayin ƙungiya ta 12. Sun tsallake zuwa zagaye na uku na gasar, kafin daga bisani kungiyar Alvaro Robles ta Spaniya da Galia Dvorak (1-4) ta fitar da su.
Wasannin Afirka duka (All-African Games)
Assar ya lashe wasanni biyu na shekarun 2015 da 2016 na Afirka baki daya, na maza. A cikin shekarar 2017, dan wasan table tennis na Najeriya, Quadri Aruna, ya katse masa peat uku, wanda ya doke Assar a wasan karshe (3-4).
2018 ITTF Kofin Afirka
Assar ya doke dan wasan tennis na Tunisia Thameur Mamia da ci 4-1 a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar. Sannan ya doke Saheed Idowu a wasan kusa da na karshe (4-0). A karshe Assar ya doke Quadri Aruna wanda ya dade yana hammaya a wasan karshe a gasar domin ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na uku.
2020 Olympics
A gasar Olympics ta lokacin zafi ta 2020, Assar ya zo na 5 a gasar men's singles bayan da ya sha kashi a hannun Ma Long na kasar Sin a wasan daf da na kusa da na karshe.[4] Ya kuma fafata a gasar qungiyar ta maza da mixed doubles.[5]
Tun daga watan Agusta 2021, Omar yana matsayi na 36 a duniya a cikin ITTF na duniya. Ya kai matsayi mafi girma na 16th a cikin watan Maris 2016.[6]