Palmira Barbosa | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
District: National Constituency of Angola (en) | |||||||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Luanda, 25 Nuwamba, 1961 (63 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Angola | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | handball player (en) da ɗan siyasa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||||||
Jam'iyar siyasa | People's Movement for the Liberation of Angola (en) |
Palmira Leitão de Almeida Barbosa, wanda ake yi wa lakabi da Mirita, (an haife ta ranar 25 ga watan Nuwamba 1961) 'yar wasan ƙwallon hannu ce ta kasar Angola. Ta fara aikinta a Clube Ferroviário de Luanda a cikin shekarar 1980s kuma a cikin shekarar 1996 ta koma Petro Atlético.[1] Ta shiga cikin tawagar kwallon hannu ta Angola a shekarar 1980, inda ta fara shiga gasar cin kofin duniya a Koriya ta Kudu a shekarar 1990. Tun daga nan ta sake buga gasar cin kofin duniya uku. A watan Fabrairun 2000, tana da shekaru 39, ta sanar da yin ritaya da kuma sha'awarta na neman aikin horarwa. Daga baya ta sake duba ta kuma taka leda har sau biyu tare da sabuwar kungiyar da aka kafa ta ENANA.[2]
A tsawon rayuwarta ta lashe gasar zakarun kulob-kulob na Afirka 8 tare da Petro Atlético, Gasar Cin Kofin Afirka 4 na Angola, kofunan wasannin Afirka guda 3, da kuma shiga gasar cin kofin duniya 4 da wasannin Olympic 1 ( 1996 ).
A shekarar 1998, Hukumar Kwallon hannu ta Afirka ta zabe ta mafi kyawun 'yar wasan kwallon hannu na mata a kowane lokaci.[3]
A halin yanzu ita 'yar majalisa ce ta jam'iyyar MPLA mai mulki.
Bayan zaben Angola a 2022 an nada ta a matsayin ministar wasanni da matasa.[4]