Pape Latyr N'Diaye | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Ouakam (en) , 30 Nuwamba, 1977 (46 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Senegal | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai tsaran raga |
Pape Latyr N'Diaye (an haife shi ranar 30 ga watan Nuwamban 1977), tsoho ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a matsayin mai tsaron gida.[1]
An haife shi a Ouakam, N'Diaye ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar Entente Sotrac a cikin shekara ta (1993).[2] Ya koma AS Douanes a shekara ta (2002), inda zai lashe gasar cin kofin FA na Senegal sau uku a jere.[2]
N'Diaye ya ƙulla yarjejeniya da US Ouakam a (2006), kuma ya zama kaftin ɗin ƙungiyar da ta lashe Kofin FA na Senegal a (2006),[3] da kuma gasar Premier ta Senegal ta 2011 - gasar farko ta ƙungiyar a tarihinta na shekaru 60.[4]
N'Diaye bai buga wa tawagar ƙasar Senegal ba, amma an kira shi don wasan sada zumunci da Benin a ranar 7 ga watan Fabrairun (2007).[5] Ya kasance mai tsaron gida da ba a yi amfani da shi ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta (2012),[6] shi kaɗai ne ɗan wasan da ya taka leda a gasar cikin gida.[7]