![]() | |||
---|---|---|---|
1 ga Yuli, 2014 - 1 ga Yuli, 2019 District: North East England (en) ![]() Election: 2014 European Parliament election (en) ![]() | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Peterborough, 13 Satumba 1962 (62 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Leeds (en) ![]() | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Wurin aiki |
Strasbourg da City of Brussels (en) ![]() | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Labour Party (en) ![]() |
Paul Brannen (an haife shi ranar 13 ga watan Satumba, 1962) ɗan siyasa ne a karkashin Jam'iyyar Labour ne na Biritaniya. Shi tsohon memba ne na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) na yankin Arewa maso Gabashin Ingila : an zaɓe shi a 2014 kuma ya rasa kujerarsa a 2019.
Brannen ya tashi a Tyneside, Arewa maso Gabashin Ingila.[1] Ya halarci Jami'ar Leeds, inda ya karanta tiyoloji da karatun addini. Kasancewa cikin siyasar ɗalibai, ya zama Shugaban Ƙungiyar Jami'ar Leeds.[2] Brannen kuma yana da MBA daga Makarantar Kasuwancin ta Jami'ar Durham.[3]
Bayan kammala jami'a, Brannen ya yi aiki da kungiyar Anti-Apartheid Movement, inda ya jagoranci gangamin yaki da kisa daga gwamnatin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Ya shahara wajen katse taron manema labarai da Mike Gatting yake yi domin bayyana shirinsa na jagorantar rangadin wasan kurket na 'yan tawaye zuwa kasar Afirka ta Kudu, wanda ya sabawa kauracewa wasannin kasa da kasa. Daga baya ya koma Christian Aid, inda ya jagoranci yakin neman kamfe kan talauci da kuma, kwanan nan, sauyin yanayi. Brannen ya yi shekaru biyar a matsayin Kansila a Majalisar Birnin Newcastle . Sau biyu yana tsayawa takarar dan majalisa ; don Berwick-kan-Tweed a cikin 1997, da na Hexham a 2001. Bai yi nasara ba a zabukan biyu bayan ya zo na biyu.[2][4]
Brannen ya tsaya takara a zaben Majalisar Turai na 2014 a matsayin dan takarar jam'iyyar Labour a yankin Arewa maso Gabashin Ingila.[5] A yayin da jam'iyyar Labour ta lashe mafi yawan kuri'u a yankin, Ya zamo dan majalisar Tarayyar Turai.[6] A ranar 1 ga watan Yuli, 2014, an zaɓe shi a kwamitin noma da raya karkara.[7]
Ya goyi bayan Owen Smith a zaɓen shugabancin jam'iyyar Labour (Birtaniya) a shekarar 2016.[8]