Paulin Soumanou Vieyra | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Porto-Novo, 31 ga Janairu, 1925 |
ƙasa |
Benin Senegal Faransa |
Mutuwa | Faris, 4 Nuwamba, 1987 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Myriam Warner-Vieyra |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta | Institut des hautes études cinématographiques (en) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, filmmaker (en) da mai sukar lamarin finafinai |
IMDb | nm0896895 |
Paulin Soumanou Vieyra, (31 Janairu 1925 - 4 Nuwamba 1987) darektan fina-finan Dahomeyan/Senegal ne kuma masanin tarihi. Yayin da ya zauna a ƙasar Senegal bayan ya kai shekaru 10, an fi danganta shi da wannan al'ummar.
An haife shi a Porto Novo, Dahomey, kuma ya yi karatu a ƙasar Paris, Faransa, [1] inda ya yi karatu a Institut des hautes études cinématographiques. A cikin shekarar 1955 a Paris,[2] inda yayi karatu a Institut des hautes études cinématographiques.[3] ya nuna fim ɗin Afirka na farko, Afrique-sur-Seine. Sauran muhimman nasarorin da ya samu na fim a Afirka sun haɗa da kafa Fédération Panafricaine des Cinéastes a 1969. Ya yi aiki a matsayin darekta na Actualités Sénégalaises, muhimmin sabis na labarai a cikin shekaru ashirin bayan samun yancin kai na Senegal.[4]
A shekara ta 1971, ya kasance mamba na juri a 7th Moscow International Film Festival.[5] Bayan shekaru biyu, ya kasance mamba na juri a 8th Moscow International Film Festival. A shekarar 1985 ya kasance memba na juri a 14th Moscow International Film Festival.[6]
Ya mutu a Ƙasar Paris a shekarar 1987, yana da shekaru 62. [7]
A cikin shekarar 1961, ya auri mawakiya Myriam Warner na Guadeloupe. Ɗaya daga cikin 'yan uwansa Justine Vieyra, haifaffen Parakou.