Peride Celal | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Istanbul, 10 ga Yuni, 1916 |
ƙasa | Turkiyya |
Mutuwa | Istanbul, 17 ga Yuni, 2013 |
Makwanci | Zincirlikuyu Cemetery (en) |
Karatu | |
Makaranta | Q653070 |
Harsuna | Turkanci |
Sana'a | |
Sana'a | author (en) |
IMDb | nm0147924 |
Peride Celal Yönsel (10 ga Yuni, 1916 - 15 ga Yuni, 2013), wanda aka fi sani da Peride Celal ko Peride Celâl ɗan Turkiyya ne, Marubuciyar labarai.
An haifi Celal a cikin İstanbul, daular Usmaniyya a ranar 10 ga Yuni, 1916. Ta kammala karatunta na makarantar sakandare a Samsun da kuma tsarin karatun Faransa a Lycée Saint Pulchérie a İstanbul . Celal ta yi mafi yawan yarintar ta a Anatolia . Tana da 'ya ɗaya, Zeynep Ergun .
Peride Celal ta mutu a ranar 15 ga Yuni, 2013, amma bayan kwana biyu sai dangin ta suka sanar da hakan.
A shekarar 1977, an karrama ta ne saboda littafinta Üç Yirmi Dört Saat tare da lambar girmamawa ta Adabin Sedat Simavi na Turkiyya tare da Fazıl Hüsnü Dağlarca . Kyautar Noha ta 1991 Orhan Kemal Novel an ba Peride Celal don littafinta Kurtlar .
A shekarar 1996, Selim İleri ya wallafa wani littafi mai suna Present to Peride Celal (Peride Celal'e Armağan) wanda marubutan Turkawa 19 suka shirya.