Philip A. Traynor | |||||
---|---|---|---|---|---|
3 ga Janairu, 1945 - 3 ga Janairu, 1947 ← Earle D. Willey - J. Caleb Boogs (en) → District: Delaware's at-large congressional district (en)
3 ga Janairu, 1941 - 3 ga Janairu, 1943 ← George S. Williams - Earle D. Willey → District: Delaware's at-large congressional district (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Wilmington (en) , 31 Mayu 1874 | ||||
ƙasa | Tarayyar Amurka | ||||
Mazauni | Wilmington (en) | ||||
Mutuwa | Wilmington (en) , 5 Disamba 1962 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Delaware (en) University of Pennsylvania School of Dental Medicine (en) Goldey–Beacom College (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da dentist (en) | ||||
Wurin aiki | Washington, D.C. | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Democratic Party (en) |
Philip Andrew Traynor (An haife shi ranar 31 ga watan Mayu, 1874 - 5 ga Disamba, 1962) ya kasance likitan hakora na Amurka kuma ɗan siyasa daga Wilmington, a New Castle County, Delaware . Ya kasance memba na Jam'iyyar Democrat kuma ya yi aiki sau biyu a matsayin Wakilin Amurka daga Delaware .
An haifi Traynor a Wilmington, Delaware . Ya halarci makarantun jama'a, Kwalejin Kasuwanci ta Goldey, a Wilmington, da Jami'ar Delaware a Newark . Ya kammala karatu a shekara ta alif dari takwas da casain da biyar 1895 daga sashen haƙori na Jami'ar Pennsylvania a Philadelphia, kuma ya fara aikin haƙori a Wilmington.
Traynor ya kasance memba na kwamitin likitan hakora na Delaware daga shekara ta alif dari tara sha takwas 1918 har zuwa shekara ta alif dari tara da arbain da uku 1943, yana aiki a matsayin shugabanta bayan ya dauki lokaci tun daga shekara ta alif dari tara da ashirin da biyu 1922. Ya kuma kasance mataimakin shugaban kasa kuma memba na kwamitin amintattu na Makarantar Masana'antu ta Ferris daga shekarar alif dari tara da talatin da takwas 1938 har zuwa shekarar alif dari tara da arbain da biyu 1942. An zabe shi a Majalisar Wakilai ta Amurka a shekarar alif dari tara arbain 1940, inda ya kayar da wakilin Jamhuriyar Republican na Amurka George S. Williams. Ya rasa yunkurinsa na karo na biyu a shekarar alif dari tara da arbain da biyu 1942 ga dan jam'iyyar Republican, Earle D. Willey, amma a cikin wani wasa na shekara ta alif dari tara da arbain da hudu 1944 ya ci Willey. A ƙarshe, ya rasa takararsa na karo na uku ga Jamhuriyar Republican J. Caleb Boggs, lauyan New Castle County, kuma tsohon soja. Traynor ya yi aiki a cikin mafi rinjaye na Democrat a Majalisa ta 77 da 79. Ya kasance a ofis daga watan Janairu 3, na shekara ta alif dari tara da arbain da ɗaya 1941, har zuwa Janairu 3, 1943, kuma daga Janairu 3 1945, har zuwa ranar uku 3 ga watan Janairun shekara ta alif dari tara da arbain da bakwai 1947, a lokacin gwamnatocin shugabannin Amurka Franklin D. Roosevelt da Harry S. Truman .[1]
Traynor ya mutu a Wilmington, kuma an binne shi a Kabari na Cathedral a can.
Ana gudanar da zabe a ranar Talata ta farko bayan Nuwamba 1. Wakilan Amurka sun fara aiki a ranar 3 ga watan Janairu kuma suna da wa'adin shekaru biyu.