Potato Potahto (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2017 |
Asalin harshe | Turanci |
Ƙasar asali | Najeriya da Ghana |
Distribution format (en) | video on demand (en) |
Characteristics | |
Genre (en) | comedy film (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Shirley Frimpong-Manso |
'yan wasa | |
External links | |
Specialized websites
|
Potato Potahto fim ne na barkwanci na soyayya na kasashen Ghana da Najeriya na shekarar 2017 wanda ke ba da labarin sakin aure a yammacin Afirka.[1][2]
Potato Potahto wani fim ne na barkwanci tsakanin Ghana da Najeriya, wanda ya biyo bayan rayuwar wasu ma'auratan da aka tilasta musu zama tare a gida ɗaya bayan rabuwar aure.[3][4]
Fim ɗin haɗin gwiwa ne na kamfanonin Najeriya Ascend Studios, 19 April Entertainment Virgo Sun Ltd da Lufodo Productions kuma mai shirya fina-finan Ghana, Shirley Frimpong-Manso ne ya ba da Umarni shirin. Ya ba da labarin abubuwa masu ban haushi da ke faruwa sa’ad da ma’auratan da suka rabu suka zauna tare a gidan aure, kowannensu yana samun taimakon matasa masu ban sha’awa daga kishiyoyi. An ɗauki fim din ne a cikin tsawon makonni biyu, tare da kokarin hadin gwiwa daga masu shirya fina-finai na Sweden, Faransa, Birtaniya, Najeriya da Ghana.
Potato Potahto ya samu karɓuwa daga jama'a, saboda nasarar da Shirley Frimpong-Manso ya samu a baya. Masu amfani da fim ɗin sun bashi kashi 7.9 akan Nollywood Reinvented. An nuna shirin a bukukuwan Cannes Film Festival, Durban International Film Festival da Birtaniyya Film Festival. Fim ɗin ya kuma fito a matsayin wani ɓangare na zabubbukan da za a yi a bikin Fina-finan Afirka daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 5 ga Nuwamba. A watan Disamba na shekara ta 2019, an ɗora fim ɗin a hukumance acikin kundin fina-finai akan dandalin Netflix.[5][6]
Kyauta | Iri | Recipients and nominees | Sakamako | Madogara |
---|---|---|---|---|
Toronto Nollywood International Film Festival | Best Feature Film (Nollywood) | Potato Potahto | Lashewa | [7] |
Best Costume | Potato Potahto | Lashewa | ||
Special Jury Awards for Best Actor | OC Ukeje | Lashewa | ||
Best Actor in a Supporting Role (English) | Chris Attoh | Ayyanawa | ||
Best Actress | Joselyn Dumas | Lashewa | ||
Africa Magic Viewers’ Choice Awards | Best Actor in a Comedy | OC Ukeje | Ayyanawa | [8] |
Best Cinematography | Kwame Amuah | Ayyanawa | ||
Best Movie West Africa | Potato Potahto | Ayyanawa | ||
Best Director | Shirley Frimpong-Manso | Ayyanawa | ||
Best Overall Movie | Potato Potahto | Ayyanawa | ||
Best Costume Designer Movie or TV Series | Christie Brown | Ayyanawa | ||
Africa Movie Academy Award | Best Actress in a Supporting Role | Joke Silva | Lashewa |