Qasim al-Raymi

Qasim Yahya Mahdi al-Raymi (Samfuri:Langx; an haifeshi a ranar 5 ga watan Yuni shekarata alif 1978 zuwa ranar 29 ga watan Janairu shekarata 2020) ya kasance ɗan gwagwarmayar Yemen wanda ya kasance sarkin al-Qaeda a yankin Larabawa (AQAP).[1] Al-Raymi na ɗaya daga cikin mutane 23 da suka tsere acikin kurkuku na 3 ga Fabrairu 2006 a Yemen, tare da wasu sanannun mambobin al-Qaeda. Al-Raymi yana da alaƙa da fashewar bam na watan Yuli shekarata 2007 wanda ya kashe masu yawon bude ido takwas na Spain. Bayan ya yi aiki a matsayin kwamandan soja na AQAP, an kara al-Raymi zuwa jagora bayan mutuwar Nasir al-Wuhayshi a ranar 12 ga watan Yuni shekarata 2015.

  1. "AQAP confirms death of senior leader". The Long War Journal. 16 June 2015. Retrieved 12 May 2016.