Rachid Benhadj | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Rachid Mohamed |
Haihuwa | Aljir, 12 ga Yuli, 1949 (75 shekaru) |
ƙasa | Aljeriya |
Sana'a | |
Sana'a | darakta da marubin wasannin kwaykwayo |
IMDb | nm0071123 |
Mohamed Rachid Benhadj (Larabci: رشيد بن حاج, an haife shi a ranar 12 Yuli 1949) darektan fina-finan Aljeriya ne kuma marubucin allo.
An haife shi a Algiers, Benhadj ya karanci gine-gine da cinema a Jami'ar Paris.[1] Ya fara aikin sa na ƙwararru yana aiki da Radiodiffusion Télévision Algérienne a matsayin ɗan jarida.[2] Fim ɗin sa na farko Louss (aka Desert Rose, 1989) ya sami yabo mai yawa.[3][4] A cikin shekarar 1990s ya yanke shawarar zama na dindindin a Italiya. Ya fara daga fim ɗinsa na biyu Touchia Fina-finansa sun kara himma wajen kyautata zamantakewa da siyasa. Shi ma mai zane ne.