Rachmat Witoelar | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tasikmalaya (en) , 2 ga Yuni, 1941 (83 shekaru) |
ƙasa | Indonesiya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Erna Witoelar (en) |
Karatu | |
Makaranta |
Bandung Institute of Technology (en) Canisius College (en) |
Harsuna | Indonesian (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya |
Mahalarcin
| |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Golkar (en) |
Rachmat Nadi Witoelar Kartaadipoetra ko Rachmat Witoelar (an haife shi 2 Yunin shekarar 1941 a Tasikmalaya, West Java ) ɗan siyasa ne wanda ya yi aiki a matsayin Ministan Muhalli na Indonesia a 2004-2009.
Witoelar ya kammala karatun digiri a fannin gine-gine daga Cibiyar Fasaha ta Bandung (ITB) a cikin 1970. A 1971, ya zama ɗan majalisa mai wakiltar jam'iyya mai mulki, Golkar . An sake zaɓe shi sau huɗu. A cikin shekarar 2004, ya zama memba mai ƙwazo na ƙungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa Susilo Bambang Yudhoyono . Lokacin da aka zaɓi Yudhoyono a matsayin shugaban ƙasa, an naɗa Witoelar ƙaramin ministan muhalli.
Rachmat ya rike mukamai daban-daban a majalisar wakilai, ciki har da shugaban majalisar wakilai V da Commission VI. Ya kuma kasance babban sakataren jam'iyyar Golkar daga 1988 zuwa 1993. Ya yi aiki a matsayin jakadan Indonesia a Rasha da Mongoliya daga 1993 zuwa 1997.
Witoelar ya auri Erna Witoelar . Suna da 'ya'ya maza uku. An kuma zaɓi Witoelar a matsayin shugaban Majalisar Dinkin Duniya Tsarin Sauyin Yanayi (UNFCCC 2007) na goma sha uku wanda aka gudanar a Bali, Indonesia.
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |