Raphaël Adicéam

Raphaël Adicéam
Rayuwa
Haihuwa Argenteuil (mul) Fassara, 1990 (34/35 shekaru)
ƙasa Faransa
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Raphaël Adicéam[1] (an haife shi ranar 3 ga watan Yuli a shekarar 1990) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na Faransa wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida a ƙungiyar kwallon kafar Auxerre a Ligue 1 na Faransa.[2]

Yayin wasa a kungiyar Amiens, Adicéam ya fara wasansa na ƙwararru a cikin wasan da sukai rashin nasarar 2–1 Coupe de la Ligue zuwa Clermont a ranar 9 ga watan Agustan 2016.[3]

A ranar 3 ga Janairu 2022, Adicéam ya rattaba hannu kan kungiyar Championnat National 2 Beauvais.[4]

A ranar 21 ga Satumba 2023, Adiceam ya koma Auxerre har zuwa ƙarshen kakar wasa.