Rebecca Nyandeng De Mabior | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
21 ga Faburairu, 2020 -
2020 -
2005 - 2011
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Bor (en) , 15 ga Yuli, 1956 (68 shekaru) | ||||||||
ƙasa |
Sudan ta Kudu Sudan | ||||||||
Ƙabila | Dinka people (en) | ||||||||
Ƴan uwa | |||||||||
Abokiyar zama | John Garang (en) | ||||||||
Yara |
view
| ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Mamba |
Southern Sudan Autonomous Region (en) Sudan People's Liberation Army (en) | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Sudan People's Liberation Movement (en) |
Rebecca Nyandeng De Mabior (an haife Rebecca a ranar 15 ga watan Yulin shekara ta 1956) [1] 'yar siyasar Sudan ta Kudu ce wacce ta rike matsayin Mataimakiyar Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ta huɗu.[2][3] Ta yi aiki a matsayin Ministan Hanyoyi da Sufuri na Gwamnatin cin gashin kanta ta Kudancin Sudan, kuma a matsayin mai ba da shawara ga Shugaban Sudan ta Kudu kan jinsi da haƙƙin ɗan adam daga 2007 zuwa 2014.[4][1] Ita ce matar marigayi John Garang, marigayi Mataimakin Shugaban Sudan na farko kuma Shugaban Gwamnatin Sudan ta Kudu, kuma mahaifiyar Akuol na Mabior . [5] Ta fito ne daga Ƙabilar Dinka ta Twic Gundumar Gabas ta Sudan ta Kudu.[6]
An haifi Rebecca a ranar 15 ga Yulin 1956 a garin Bor. A shekara ta 1986 ta yi tafiya zuwa Cuba don samun horar da soja.[1]
Bayan mutuwar Dokta John Garang, Janar Salva Kiir ya maye matsayinsa kuma ya zama Mataimakin Shugaban Sudan na farko kuma Shugaban Gwamnatin Sudan ta Kudu kuma babban kwamandan SPLM / A. Janar Kiir ya nada Rebecca Nyandeng De Mabior a matsayin Ministan Hanyoyi da Sufuri a Gwamnatin Sudan ta Kudu.
Ta ci gaba da kasancewa mai iko wajen aiwatar da Yarjejeniyar Zaman Lafiya wanda Dr. John Garang ya sanya hannu kafin mutuwarsa a ranar 30 ga Yuli 2005. Ta ci gaba da tallafawa aiwatar da tsarin zaman lafiya har lokacin da Kudancin kasar ta samu 'yancin kai a ranar 9 ga Yulin 2011. A wannan shekarar lokacin da mijinta ya mutu Madam Rebecca ta ziyarci Amurka kuma ta gana da Shugaba George W. Bush . Ta ba da saƙon godiya ga shigar Amurka cikin neman zaman lafiya a Sudan ta Kudu. A shekara ta 2009 Shugaba Obama ya ci gaba da wannan yunkuri shi da Sakatare Clinton da Jakadan Rice don ganin cewa an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan.
Madam Rebecca kuma ta samu yin hira da NPR. Ta yi magana game da jajircewarta ga 'yancin Sudan ta Kudu yayin da take girmama bukatar haɗin kan Sudan baki daya a karkashin Sabuwar Mahangar Sudan wanda Dokta John Garang ya kirkira a 1983. Ta ziyarci Kwalejin Grinnell da kuma Jami'ar Jihar Iowa, jami'o'in Iowa inda marigayi mijinta ya kammala karatunsa kafin Yaƙin basasar Sudan na Biyu ya ɓarke a 1983. [7] Marigayi Dokta John Garang da matarsa Rebecca suna da 'ya'ya shida waɗanda ke goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali a sabuwar Jamhuriyar Sudan ta Kudu.
<ref>
tag; name "bio" defined multiple times with different content