![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa |
Okemesi (en) ![]() |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Marubiyar yara, edita da marubuci |
Muhimman ayyuka |
Moonlight Stories (en) ![]() |
Remi Aduke Adedeji (an haifeta a shekarar 1937) marubuciyar littafin Yara ce a Najeriya.
An haifi Adedeji a Okemesi a jihar Ekiti a shekarar 1937.[1] Adedeji ta ji takaicin littattafan Yara da ba su nuna al'adun Afirka ba. Yawancin labaranta sun samo asali ne daga tatsuniyoyi na Najeriya. [1] Ta rubuta gami da buga littafin The fat woman (Mata mai ƙiba) a shekarar 1973.[2] Ta zama editan ga mujallar ilimi, Bookbird.[3] Littattafanta akai-akai sun ƙunshi dabi'un kunkuru (dabba kunkuru). Littafinta na (Moonlight Storie)-"Labarun Hasken Wata" na 1986 ya ƙunshi labarai da dama da suka bayyana dalilin da yasa ungulu ke da gashi ko kuma dalilin da yasa ƙoƙon kunkuru ya bayyana.[4]