Richard Kissi Boateng | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Accra, 25 Nuwamba, 1988 (36 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ghana | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa |
Mai buga baya fullback (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 27 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 183 cm |
Richard Kissi Boateng[1] (an haife shi a ranar 25 ga watan Nuwambar 1988), ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Ghana wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin ɗan baya na hagu don Berekum Chelsea .
Boateng ya fara aikin samartaka ne da ƙungiyar Saint Stars FC, kafin daga baya ya koma Liberty Professionals FC a shekara ta 2004, inda ya fara babban aiki da kwararre. A cikin shekarar 2008, an zaɓe shi a matsayin mai tsaron gida na shekara a Ghana.[2] A cikin watan Yulin 2010, ya koma Al-Ittihad ta Libya, kuma ya koma Ghana don Berekum Chelsea a watan Satumba 2011. A ranar 16 ga watan Janairun 2013, Boateng ya rattaba hannu a kulob ɗin TP Mazembe na Congo kan yarjejeniyar shekaru biyar. [3]
A cikin watan Janairun 2020, Boateng ya koma Berekum Chelsea . [4]
A ranar 16 ga watan Mayun 2012, an kira Boateng zuwa tawagar Ghana don wasanni biyu, 2014 na cancantar shiga gasar cin kofin duniya da kungiyar kwallon kafa ta Lesotho ta kasa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zambiya .[5]
Boating ya yi aure a shekarar 2014. Shi da matarsa sun yi maraba da ɗa a shekarar 2017.