Richard Mbulu | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Mangochi (en) , 25 ga Janairu, 1994 (30 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Tsayi | 1.85 m |
Richard Mbulu (an haife shi a ranar 25 ga watan Janairun 1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Malawi wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a ƙungiyar Baroka ta Afirka ta Kudu. An saka shi cikin tawagar `yan wasan Malawi a gasar cin kofin Afrika na 2021.[1]
An haifi Mbulu a Mangochi, Malawi.[2]
Bayan ya fara aikinsa a Kwalejin Sojojin Malawi bayan shiga aikin soja,[3] ya koma Costa do Sol ta Mozambique a watan Disamba 2016.[4] Daga baya ya koma kungiyar AD Sanjoanense ta Portugal kafin ya koma Costa do Sol a lokacin bazara na 2018.[5] A lokacin bazara na 2019, Mbulu ya rattaba hannu a kungiyar Baroka ta Afirka ta Kudu kan yarjejeniyar shekaru uku.[6]
An kira shi zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Malawi a karon farko a cikin Janairu 2017,[7] kuma ya fara buga musu wasa a ranar 10 ga watan Yunin 2017 a 1-0 da Comoros ta yi nasara.[1] Ya ci kwallonsa ta farko a Malawi a ranar 4 ga watan Satumba 2017 a ci 1-0 da Togo.[8] Ya zura kwallo daya tilo a wasan da ta doke Uganda da ci 1-0 wanda ya baiwa Malawi damar tsallakewa zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka na 2021.[9]
Lokacin da Mbulu ya bar makaranta, ya zama soja amma daga baya ya yanke shawarar yin sana’ar kwallon kafa. Mahaifinsa kuma dan wasan kwallon kafa ne kuma soja.[10][3]