![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
1 ga Yuni, 2013 - District: NA-102 (Hafizabad-I) (en) ![]()
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa |
Hafizabad (en) ![]() | ||||
ƙasa | Pakistan | ||||
Harshen uwa | Urdu | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of the Punjab (en) ![]() | ||||
Harsuna | Urdu | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Mahalarcin
| |||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa |
Pakistan Muslim League (N) (en) ![]() |
Saira Afzal Tarar ( Urdu: سائرہ افضل تارڑ; an haife ta a ranar 7 ga watan Yunin 1966), ƴar siyasan Pakistan ce wadda ta yi aiki a matsayin Ministan Kula da Ayyukan Kiwon Lafiya na ƙasa, a cikin majalisar Abbasi daga watan Agustan 2017 zuwa watan Mayun 2018. Ta yi aiki a matsayin ƙaramar ministar kula da harkokin kiwon lafiya ta ƙasa daga shekarar 2013 zuwa ta 2017. Shugabar ƙungiyar Musulmi ta Pakistan (Nawaz), ta kasance mamba a Majalisar Dokokin Pakistan daga shekarar 2008 zuwa watan Mayun 2018.
An haife ta a ranar 7 ga watan Yunin 1966 [1] a Hafizabad, Punjab, Pakistan .[2]
An zaɓi Tarar a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ƴar takarar Pakistan Muslim League (N) (PML-N) daga Mazaɓar NA-102 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 .[3]
An sake zaɓen ta a Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin 'yar takarar PML-N daga Mazaɓar NA-102 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 .[4][5]
A cikin watan Yunin 2013, an naɗa ta a matsayin ministar lafiya a majalisar ministocin Firayim Minista Nawaz Sharif .[6][7][8][9] Ta daina riƙe mukamin minista a watan Yulin 2017 lokacin da aka rusa majalisar ministocin tarayya sakamakon rashin cancantar firaministan ƙasar Nawaz Sharif bayan yanke hukuncin shari'ar Panama Papers .[10]
Bayan zaɓen Shahid Khaqan Abbasi a matsayin Firayim Minista na Pakistan a watan Agustan 2017, an shigar da ita cikin majalisar ministocin gwamnatin Abbasi .[11][12] An naɗa ta ministar kula da harkokin kiwon lafiya ta tarayya. [13] Bayan rusa majalisar dokokin ƙasar a kan ƙarewar wa’adinta a ranar 31 ga watan Mayun 2018, Tarar ta daina riƙe mukamin ministan kula da harkokin kiwon lafiya ta tarayya.[14] A cikin watan Maris 2018, ta karɓi Sitara-i-Imtiaz don hidimar jama'a ta Shugaban Pakistan, Mamnoon Hussain .[15]