![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Wa, 14 Disamba 1989 (35 shekaru) |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta |
Odorkor '1' Primary (en) ![]() University of Ghana |
Matakin karatu |
undergraduate degree (en) ![]() |
Harsuna |
Turanci Yaren Akan |
Sana'a | |
Sana'a |
jarumi, mai tsara fim da entrepreneur (en) ![]() |
Muhimman ayyuka |
Passion and Soul (en) ![]() The Will (en) ![]() John and John (fim) College Girls (en) ![]() No Man's Land (en) ![]() Apples and Bananas (en) ![]() Seduction (en) ![]() |
Kyaututtuka |
gani
|
IMDb | nm4449764 |
Salma Mumin ta kasance yar kasar Ghana ce ,kuma mai shirin fim.[1] Aikace aikacenta a kamfanin fim din kasar ta ya janyo mata lashe kyautuka da dama, wanda suka hada da Best International New Actress a shekarar 2014, Papyrus Magazine Screen Actors Awards da kuma Best Actress a shekarar 2019, Ghana Movie Awards.[2][3]
Salma Mumin an haife ta a Wa, acikin Yankin Yammacin Upper na Ghana Kuma anan ne ta gudanar da yawancin rayuwan yarintar ta. Ta yi makarantar Odorkor 1 Primary School sannan tayi makarantar Insaaniyya Senior Secondary School.[4] daga baya ta koma accra domin chigaba da aikin fina-finai
.[5]
Mumin ta fara aikin shirin fim a shekarar 2007, inda ta fito acikin fim din Passion and Soul.[6] Tun shekarar 2012, ta rika fitowa a fina-finai kamar su Seduction, No Apology, College Girls, Leave my wife, The Will, No Man’s Land, da What My Wife Doesn’t Know, da kuma John and John.[7] fina-finan ta na farko su ne I Love Your Husband 1, 2, da na 3 a shekarar 2009. Ta kuma fito a film din You May Kill the Bride a shekarar 2016.
A shekarar 2015, gudanar da shirin ta na farko a No Man's Land.[8]
Ana ganin fuskokin Mumin a Manyan allunan talla da tallace-tallacen TV a Ghana, wadanda suka hada da talla ga kamfanonin kamar UniBank, Jumbo, Electromart da sauraran su. Tallan ta na farko a TV shine na UniBank. Kuma itace jakadiyar tallace-tallace na Hollywood Nutritions Slim Smart.[9]